A jiya Litinin ne daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Sin, kuma daraktan kasar Sin a hukumar gudanarwar IAEA Zhang Kejian, ya halarci taron IAEA na watan Yunin nan a birnin Vienna tare da gabatar da jawabi.
Cikin jawabin nasa, Zhang Kejian ya soki lamirin kasar Japan, na shirin zubar da dagwalon nukiliyar Fukushima cikin teku.
Zhang Kejian ya ce batun shigar da wannan gurbataccen ruwa cikin teku, muhimmin lamari ne da ya shafi harkokin muhallin tekunan duniya, da fannin kiwon lafiyar daukacin al’ummun kasa da kasa, ba wai batu ne da ya shafi kasar Japan kadai ba.
Don haka jami’in ya yi kira ga gwamnatin Japan, da ya mayar da hankali ga damuwar kasashen duniya, ta kuma sauke nauyin dake wuyanta na kare hakkokin al’ummar duniya.
Zhang Kejian ya ce ya kamata Japan din ta bi hanyoyi na kimiyya, a fayyace kuma marasa hadari, wajen kawar da dagwalon na Fukushima, tare da amincewa da sanya idon sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp