Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Habu Muhammad Fagge a matsayin shugaban gudanarwa na hukumar fansho ta jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata.
- Bangaren Samar Da Hidima Na Sin Ya Sake Farfadowa A Mayu
- Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Nada Masu Bashi Shawara 20
Nadin ya fara aiki ne nan take kamar yadda gwamnan ya bayar da umarnin karbar ragamar aikin hukumacikin sa’o’i 24.
Alhaji Habu Fagge, wanda ya kammala karatunsa a fannin sha’anin Kudi a Jami’ar Abraham Lincoln.
Ya rike mukamai daban-daban a ma’aikatan gwamnatin Jihar Kano da suka hada da daraktan kudi, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga da daraktan a hukumar tara haraji.