Kasar Sin ta sanya hannu kan wasu takardu tare da wakilan bangaren falasdinawa, don mika rukuni biyu na kayayyakin agajin gaggawa ga falasdinawa a zirin Gaza.
A cewar ofishin jakadancin Sin dake Masar, an yi bikin sanya hannu kan takardun ne a ranar Litinin, a kan idon jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang, da jakadan falasdinu a Masar Diab al-Louh.
- Amurka Ta Lahanta Taiwan Na Kasar Sin Ta Hanyar Sayarwa Yankin Da Makamai
- Sanata Barau Ya Roƙi Ganduje Ya Ƙwato Jihohin Da Suka Yi Wa Jam’iyyar APC Tutsu
Da yake tsokaci game da hakan, jakada Liao ya ce, “domin saukaka wahalhalun da ake fuskanta a zirin Gaza, gwamnatin kasar Sin na ci gaba da gabatar da tallafi akai akai ga falasdinawa, inda a karo daban daban Sin ta gabatar da kayayyakin agajin jin kai da suka hada da abinci, da magunguna zuwa yankin na Gaza ta mashigar kasar Masar”.
A nasa tsokacin kuwa, mista Al-Louh cewa ya yi, gwamnati da al’ummar falasdinawa na matukar godiya ga tallafin da Sin ke bayarwa, da nufin sassauta mummunan yanayin matsi da ake fama da shi a zirin Gaza.
Al-Louh ya kuma jinjinawa sahihin goyon bayan yiwa falasdinawa adalci da kasar Sin ke yi, da yadda kasar ke yayata hakan a duk lokacin da ake tattauna batutuwa a matakin kasa da kasa, wanda hakan ke shaida kawancen kut da kut dake tsakanin Sin da falasdinu, da ma yadda kasar Sin ke sauke nauyin dake wuyanta a matsayin babbar kasa mai nuna sanin ya kamata. (Saminu Alhassan)