Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi karin bayani kan “shirin kasar Sin kan yin kwaskwarima da raya tsarin harkokin duniya” da aka fitar Larabar nan, a taron manema labarai da aka saba yi Larabar nan. Mao ta ce shirin ya ba da gudummawar hikimar kasar Sin wajen yin kwaskwarima ga tsarin tafiyar da harkokin duniya.
Mao ta ce, “shirin kasar Sin kan yin kwaskwarima da raya tsarin harkokin duniya”, ya yi karin haske kan matsaya da shawarwarin kasar Sin game da zaman lafiya da tsaro, da raya kasa, da kare hakkin dan Adam, da al’umma, da sauran muhimman fannonin gudanar da harkokin duniya, da yin gyare-gyare kan kungiyoyin kasa da kasa, da kuma yin kira ga kasashen duniya, da su hada kai wajen aiwatar da shawarar raya kasa da kasa, da shawarar samar da tsaro a duniya, da shawarar wayewar kan duniya, da inganta gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil Adama.
Ya nuna irin rawar da kasar Sin take takawa a matsayinta na babbar kasa da kuma rawar da take takawa a harkokin kasa da kasa. A shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da dukkan bangarori, wajen aiwatar da ra’ayin bangarori daban-daban na hakika, da ba da sabbin gudummawa ga zaman lafiya, da ci gaba da kare hakkin dan Adam a duniya baki daya.(Ibrahim)