Yau Jumma’a, kotun jama’a ta koli ta kasar Sin, da hukumar gabatar da kararraki ta koli ta kasar, da ma’aikatar tsaron jama’a, da ma’aikatar tsaron kasa, da ma’aikatar shari’a ta Sin cikin hadin gwiwa ne suka gabatar da takardar yanka hukunci ga masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin bisa laifin raba kasa, da na rura wutar neman rabuwar kasa. Kana takardar za ta fara aiki a hukunce tun daga yau ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2024.
Takardar ta nuna cewa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su dauki alhakinsu da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, a kokarin kare mulkin kai, da ‘yancin kai, da cikakken yankunan kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp