Hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta sanar yayin taron manema labarai Larabar nan cewa, ‘yan sama jannatin kasar Sin Tang Hongbo, da Tang Shengjie, da Jiang Xinlin ne za a harba a cikin kumbon Shenzhou-17, yayin da Tang Hongbo zai kasance babban kwamanda.
Mataimakin darektan hukumar CMSA Lin Xiqiang ya ce, za a harba kumbon Shenzhou-17 ne da misalin karfe 11 da mintuna 14 na safiyar gobe Alhamis, agogon Beijing na kasar Sin, daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan da ke yankin arewa maso yammacin kasar Sin. (Ibrahim Yaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp