Kamfanin hakar mai na kasar Sin CNOOC, ya sanar da gano wani babban yankin hakar mai a teku kudancin kasar, wanda ke dauke da tarin danyen mai da ya haura tan miliyan 100.
Kamfanin wanda ya sanar da hakan a Litinin din nan, ya ce sabon yankin na hakar mai da aka gano a yankin hakar mai na Huizhou 19-6, ya bude sabon babi a ayyukan da kasar Sin ke gudanarwa na hako danyen mai daga teku, kasancewarsa na farko da kasar ta gano mai tarin danyen mai a ruwa mai zurfi.
- Ana Share Fagen Gudanar Bikin Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Shigar Da Su Kasar Sin Yadda Ya Kamata
- Gwamnati Za Ta Inganta Wuraren Tarihi Domin Nishadantarwa A Duk Jihohin Nijeriya
Kazalika, a cewar CNOOC, sabon yankin na hakar mai na da nisan kilomita kusan 170 daga birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, kuma yana da matsakaicin zurfin mita 100. Bugu da kari, gwaje-gwajen da aka yi sun nuna a kullum za a iya hakar danyen mai da ya kai ganga 413, da kuma kyubik mita 68,000 na iskar gas a wurin.
Kamfanin ya kara da cewa, aikin hakar danyen mai a irin wannan wuri mai zurfi na tattare da kalubale da dama, wadanda suka hada da tsanantar zafi, da matsin iska mai tsanani, da yanayi mai sarkakiya.
A daya bangaren kuma, yanayin matattarar danyen mai irin wannan, na samar da damar yoyewarsa, wanda hakan ke sanya aikin hakar mai da iskar gas a wurin ya zama mai matukar wahala. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp