Rundunar sojin kasar Sin PLA, ta bayyana a yau Laraba cewa, ta bibiya tare da jan kunne jirgin ruwan sojin Amurka USS Benfold, bayan ya shiga yankin ruwa dake kusa da tsibiran Xisha, a tekun kudancin kasar Sin ba tare da izinin gwamnatin kasar Sin ba.
Wata sanarwa da kakakin rundunar soji ta kudancin kasar Sin, Tian Junli ya fitar, ta ce matakin na sojin Amurka, ya keta cikakken ‘yancin kasar Sin da muradunta na tsaro, da yin karan tsaye ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin Sin.
Haka kuma, ya keta dokokin kasa da kasa da ka’idojin huldar kasa da kasa. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp