A ranar 27 ga Disamba, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya kada kuri’ar amincewa da kudurin da zai ba da izinin kafa wata runduna ta kungiyar hadin kan Afirka, watau AU mai lakabin AUSSOM, da za ta yi aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya.
A kuri’ar da aka kada, kasashe 14 sun kada kur’ar amincewa, yayin da Amurka kuma ta kauracewa abin.
Kudirin ya ba da izinin kafa rundunar AUSSOM wacce za ta maye gurbin tawagar wanzar da zaman lafiya ta wucin gadi a Somaliya mai lakabin ATMIS, tare da bai wa rundunar karfin ikon tallafa wa kokarin da kasar ta Somaliya ke yi na maido da zaman lafiya mai dorewa da tabbatar da tsaro da kuma samar da tallafin jin kai.
Bayan kammala kada kuri’ar, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Sun Zhiqian, ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kungiyar AU da gwamnatin Somaliya wajen tsara yadda za a maye tsohuwar tawagar da sabuwar rundunar da za a kafa, kuma tana fatan dukkan sassan da abin ya shafa za su ci gaba da aiki tare zuwa mataki na gaba domin tabbatar da aiki nagari wajen mika ragamar sauyin da kuma dorad da nasarorin da aka samu na yaki da ta’addanci.
Bugu da kari, ya jaddada cewa kasar Sin a shirye take ta bayar da gudummawarta ga tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Somaliya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)