Daga ranar Alhamis zuwa Juma’a 16 ga wata ne, aka gudanar da babban taron kolin tattalin arziki na shekara-shekara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugabannin kasar Sin suka yanke shawarar kan sassan da za a ba da fifiko kan ayyukan raya tattalin arziki na shekarar 2023.
Da yake gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi nazari kan ayyukan tattalin arzikin kasar a shekarar 2022, tare da nazari kan halin da ake ciki a fannin tattalin arziki, da kuma tsara aikin raya tattalin arziki na shekarar 2023 dake tafe.
A yayin taron, an bayyana cewa, ana sa ran samun farfadowa da ingantuwa baki daya ta fuskar tattalin arzikin kasar a shekara mai zuwa, kuma ya zama tilas a tabbatar da kwarin gwiwar yin aiki mai kyau a fannin aikin raya tattalin arziki.
Taron ya bukaci samun daidaito a fannin tattalin arziki a matsayin abu mai muhimmanci, tare da neman ci gaba mai dorewa, da tabbatar da daidaiton tattalin arziki a shekara mai zuwa.
A cewar taron, za a ci gaba da aiwatar da manufofin kasafin kudi mai dorewa da sanya ido yadda ya kamata a shekara mai zuwa. A halin da ake ciki kuma, za a yi kokarin karfafa ikon sarrafawa da daidaita manufofi daban-daban, domin samun ci gaba mai inganci. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)