Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, ta bayyana matukar adawa da yadda Amurka ta kara wasu kamfanonin Sin 36, cikin wadanda ta sanyawa takumkumin hana sayen hajojin latironi daga kamfanonin Amurka. Ma’aikatar ta bukacin Amurka da ta gaggauta dakatar da wannan mataki na rashin adalci nan take.
Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce a shekarun baya bayan nan, Amurka na ci gaba da fakewa da batun tsaron kasa, tana yiwa harkokin cinikayya da kamfanonin Sin kudin-gworo, tare da gurgunta hada-hada ta hanyar dakile fitar da hajoji ga kamfanonin Sin dake bukatar su, lamarin da ke haifar da illa ga kamfanoni da cibiyoyi daban daban na kasar Sin, duk da cewa sassan kamfanoni da masana’atun kasashen biyu, na gudanar da musayar cinikayya yadda ya kamata, suna kuma matukar adawa da matakan gwamnatin Amurkan. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)