Babban mai binciken kudi na kasar Sin Hou Kai, ya ce an gyara kaso 94 na kura-kuran da aka gano a rahoton binciken hada hadar kudi na kasar
A cewarsa, zuwa karshen watan Satumba, aikin gyaran ya shafi jimilar kudi yuan biliyan 538 kimanin dalar Amurka biliyan 74.8.
- Mata Ku Dage Da Karatu Domin Tallafa Wa Rayuwarku Da Ta ‘Ya’yanku – Zahra’u Adam
- Yadda Hukumar Leken Asirin Burtaniya Ta Dakile Yunkurin Kisan Fafaroma
Hou Kai ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da rahaton gyaran yayin zaman zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin.
Hukumomin kasar Sin su kan fitar da rahoton binciken ne a tsakiyar shekara, sai kuma zuwa karshen shekara a fitar da rahoton gyaran kura-kuran da aka gano yayin binciken. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)