Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar.
An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna Yaogan-40 02, ya shiga da’irarsa cikin nasara.
Za a yi amfani da taurarin ne wajen gwaje-gwajen fasahohi da gano yankuna masu tasirin haduwar maganadisu da lantarki.
ADVERTISEMENT
Aikin na jiya shi ne karo na 574 da aka yi amfani da samfurin rokar Long March. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














