A yau ne da karfe 7 da minti 20 na dare, Sin ta harba taurarin dan Adam 4 na binciken yanayi samfurin Tianmu-1 na 15 zuwa na 18 zuwa sararin samaniya cikin nasara ta hanyar amfani da rokar Kuaizhou-1A daga cibiyar harbar tauraron dan Adam ta Jiuquan, sun kuma shiga falaki kamar yadda aka tsara.
Za a yi amfani da taurarin ne don samar da hidimar yanayi. Wannan shi karo na 25 da aka yi amfani da rokar Kuaizhou-1A wajen harba taurarin. (Zainab Zhang)