A yau Asabar ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na lura da yanayin bala’u a doron kasa, wanda ake sa ran zai rika samar da bayanai ga kasar Sin dangane da aukuwar bala’u daga indallahi, ta aikewa da sakwanni tsakanin sararin samaniya zuwa doron duniya.
An harba tauraron dan Adam din mai suna Zhangheng 1-02, ta amfani da rokar Long March-2D, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, da karfe 4 saura mintuna 4 agogon Beijing, ya kuma shiga da’irarsa ba tare da wata matsala ba, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta tabbatar.
Kazalika, CNSA ta ce, wannan aiki muhimmin mataki ne da Sin ta taka, a turbar nazarin yanayin doron kasa na zahiri. An sanyawa tauraron sunan wani shahararren mai kirkire-kirkire na kasar Sin, wato marigayi Zhang Heng, wanda shi ne mutum na farko a duniya, da ya kago na’urar “seismoscope” ta hasashen aukuwar girgizar kasa, shekaru sama da 1,800 da suka gabata, kuma an samar da tauraron ne da hadin gwiwar Sin da kasar Italiya. (Saminu Alhassan)