A jiya Litinin ne gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da kidayar kasa baki daya a fannin tattalin arziki. Karkashin shirin na kidaya, jami’ai miliyan 2.1 za su tattara bayanai, da rajistar mamallaka sana’o’i da rukunonin al’umma, wadanda aka shata karkashin yankunan tattara bayanai miliyan 1.16.
A cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, za a gudanar da kidayar ne cikin watanni hudu. Ana kuma gudanar da wannan kidaya ne bayan duk shekaru 5.
- Mutane Kimanin Miliyan 135 Sun Yi Yawon Shakatawa A Yayin Hutun Bikin Sabuwar Shekara A Sin
- Xi Da Kim Sun Ayyana Shekarar 2024 A Matsayin Shekarar Abokantaka Tsakanin Sin Da Koriya Ta Arewa
A watanni 6 na karshen shekarar bara ne NBS ta gudanar da ayyukan shirya tunkarar kidayar, wadda kuma a yanzu ake gudanar da ita tun daga farkon wannan shekara ta 2024. An tsara aiwatar da rajistar masu sanao’i a wuraren da suke, da tantance ingancin bayanan da aka tattara, tare da fitar da muhimman alkaluman bayanan.
A cewar shugaban hukumar ta NBS Kang Yi, kidayar ta wannan karo wadda ita ce karo na 5, za ta nazarci matsayin ci gaban tattalin arziki, tare da fayyace nagartar masana’antun Sin na kere-kere, da na bayar da hidimomi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)