A wani bangare na bikin ranar samaniya ta kasar Sin, wadda aka yi bikin ta a Litinin din nan, an gudanar da ayyuka daban daban, da shirye-shirye masu kayatarwa, ciki har da fitar da hotunan binciken duniyar Mars masu inganci na farko da kasar ta dako.
An kuma gudanar da bikin harba kumbuna albarkacin ranar samaniyar a birnin Hefei, fadar mulkin lardin Anhui na gabashin kasar, bikin da a bana aka yiwa take da “Bincikar abubuwa domin fadada ilimi, da nazartar samaniya”.
Kaza lika a yayin bikin na yau, an bayyana sakamakon binciken hadin gwiwa, na sassan kasa da kasa, na samfuran sanadaran da kumbon Chang’e-5 na Sin ya kwaso daga duniyar wata. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)