Kasar Sin ta kafa dakunan aikin samar da kayayyakin al’adun gargajiya fiye da 9,100 a fadin kasar da ya kunshi gundumomi 1,721, kamar yadda aka ruwaito daga wani taron da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar ta gudanar a birnin Longyan da ke lardin Fujian, daga ranar Lahadi zuwa Talata.
Wadannan dakuna sun samar da ayyukan yi kai-tsaye ga fiye da mutane 270,000 wadanda aka fitar daga halin-kaka-ni-ka-yi a karkashin shirin kasar Sin na kawar da talauci, inda suke samun kudin shiga fiye da yuan 36,000 duk shekara, wato kimanin dalar Amurka 5,006.
Hari ila yau, taron ya bayyana cewa, mahukuntan da abin ya shafa sun tallafa wa al’ummomin kauyuka wajen cin gajiyar al’adun gargajiya ta, da isar da kyawawan al’adun gargajiya da aka gada ga ‘yan baya, da bunkasa samar da aikin yi da samun kudin shiga, da kuma gina yankunan karkara masu samun ci gaba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp