Kasar Sin ta kafa wani kwamitin kwararru domin kara inganta fasahar kirkirarriyar basira da aka fi sani da “Artificial Intelligence (AI)” a Turance, a wani bangare na kokarin da take yi na zurfafa bunkasa sashen fasahar ta AI da kuma karfafa samar da sabbin masana’antu, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar ta bayyana a jiya Litinin.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta shafin intanet, ta kara da cewa, sabon kwamitin wanda zai yi aiki a karkashin ma’aikatar, an dora masa alhakin tsarawa da sake bitar ingancin fasahar ta AI a sassan masana’antun da ake amfani da ita.
Wannan ne dai karon farko da ma’aikatar ta kafa irin wannan kwamitin, inda yake nunar da wani sabon babi da aka bude a bangaren inganta fasahar kirkirarriyar basira ta AI. (Abdulrazaq Yahuza Jere).