Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta ba da labari a jiya Lahadi cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta kafa manya da matsakaitan yankunan ban ruwa 7,300. Inda yawan gonaki da kasar ke iya yi musu ban ruwa sun kai fadi fiye da hekta miliyan 72, wanda ya kai kashi 56% na dukkan gonakin kasar.
Tun daga lokacin da aka kira babban taron wakilan jami’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS karo na 18, wato shekarar 2012, yawan ruwan da ake amfani da shi a kowacce hektar da ba ta wuce 0.07 ba ya ragu daga kyubik mita 404 zuwa 347, kana yawan hatsin da ake samarwa a gonakin da ruwa kyubik mita 1 ke iya malala ya karu daga kilogram 1.58 zuwa 1.8. Hakan ya sa yawan hatsin da ake samarwa a gonakin da aka yi ban ruwa yana karuwa cikin dorewa bisa tabbattacen tsarin yin ban ruwa.
Jami’i mai kula da wannan aiki a ma’aikatar ya ce, har ila yau, kasar Sin ta kafa cikakken tsarin adana ruwa da gina magudanansa da janyo shi domin malalarwa a inda ake bukata da jigilar ruwa da zubar da ruwan da ya kai fiye da ake bukata da sauransu, kuma kasar za ta ci gaba da gaggauta sauran ayyukan ban ruwa a gonaki, ta yadda za ta taka rawar gani wajen samar da isashen hatsi daga bangaren gonakin da ake wa ban ruwa. (Amina Xu)