Game da rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta gabatar don gane da batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, wanda ya zargi sauran kasashe da gazawa wajen kare hakkin dan Adam, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, rahoton na Amurka, ya zargi yanayin kare hakkin dan Adam na kasashe da yankuna kimanin 200 na duniya, amma bai ambato ita kanta Amurka ba. Don haka Sin ta kalubalanci Amurka, da ta dubi kanta, ta fara da warware matsalarta a wannan fanni.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, Amurka na gabatar da rahoton kare hakkin dan Adam na shekara-shekara, amma abubuwan dake shafar kasar Sin a rahoton jita-jita ne kawai domin kulle-kullen siyasa, matakin da Sin din ba za ta amince da shi ba.
- Kasar Sin Ta Bayyana Tarin Rarar Da Take Da Shi Ta Albarkartun Mai Da Iskar Gas
- Jami’in Ma’aikatar Wajen Sin Ya Yi Tsokaci Game Da Ziyarar Sakataren Wajen Amurka A Kasar
Har ila yau, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, idan Amurka na matukar mai da hankali ga kare hakkin dan Adam, to kamata ya yi ta daidaita matsalolin bindigogi, da miyagun kwayoyi, da nuna bambancin launin fata, da keta hakkin dan Adam dake faruwa a kasar, kana ta yi la’akari da matsalolin da ta kawo wa yankuna masu fama da rigingimu, ta hanyar tsoma baki, da samar da makamai, da kuma ta da zaune-tsaye.
Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya ce, Sin na fatan Amurka za ta dakatar da rura wutar rikici, ko bata sunan wasu sassa don gane da batun Ukraine, domin hakan ba zai warware rikicin da kasar ke fama da shi ba.
Wang, ya yi tsokacin ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayoyi game da wasu rahotanni daga bangaren Amurka, masu kunshe da zargin alakar tattalin arziki da musaya tsakanin Sin da kasar Rasha. Game da hakan, Wang Wenbin ya ce, yayin da Amurka ke samar da tarin tallafi ga Ukraine, a daya bangaren ba gaira ba dalili, ta soki halastacciyar musayar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Rasha. Ya ce, “Yin hakan munafurci ne da rashin sanin ya kamata, kuma Sin na matukar adawa da hakan”.
Bugu da kari, Wang Wenbin ya yi tsokaci game da wasu rahotanni da suka fito daga kasashen Jamus da Birtaniya, game da zargin nan da wasu sassa ke yi wa kasar Sin, na “Barazanar Leken Asiri”. Yayin taron manema labarai na Talatar nan, Wang Wenbin ya ce, ko shakka babu, burin masu zarge-zargen shi ne bata sunan kasar Sin, da dakile kamfanonin kasar, da gurgunta yanayin hadin gwiwa tsakanin Sin da Turai. Kasar Sin na kira ga sassa masu ruwa da tsaki a wannan batu, da su kauracewa wannan manufa ta kulle-kullen siyasa na shafawa kasar Sin bakin fenti.(Zainab Zhang&Saminu Alhassan)