Mataimakin wakilin Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa na birnin Geneva Li Song ya yi jawabi a gun taron tattaunawa kan tasirin da mulkin mallaka ke yi wa hakkin dan Adam, wanda aka yi a taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 51, inda ya kalubalanci kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka da Birtaniya da sauransu, da su tuna da laifinsu na mulkin mallaka da kuma daukar matakai don gyara kuskurensu.
Li Song ya yi nuni da cewa, a halin yanzu da ake bin tsarin demokuradiyya a huldar kasa da kasa, bai kamata wata kasa ta nuna karfi kan sauran kasashe ba. Ya ce har yanzu, wadancan kasashen da suka taba yin mulkin mallaka, sun kira kansu masu rajin kare hakkin dan Adam. Don haka, Sin na kalubalantar kasashen da su yi watsi da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, da kuma daina siyasantar da batun kare hakkin dan Adam.
Li Song ya kara da cewa, bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, ya kamata kasashen da suka ci gaba, su dauki matakai a fanonin rage basussuka da samar da gudummawar raya kasa don taimakawa kasashen da suka taba yi musu mulkin mallaka su samu ci gaba. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp