Cibiyar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta Xi’an, reshen kwaleji na 6 na cibiyar kimiyya da fasahar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin (CASC) ta bayyana a ranar Alhamis cewa, an kammala gwajin dakika 50 na wani babban inji mai karfin tan 120 dake amfani da karfin iskar oxygen da injin roka na kananzir cikin nasara.
Dangane da muhimman bayanan da aka gabatar, masu bincike sun tabbatar da cewa, aikin injin din ya haye ka’idojin gwajin. Za kuma a gabatar da shi ne wajen amfani da rokar Long March-7 a shekarar 2023, wanda zai tabbatar da ayyukan kasar Sin masu inganci na harba kumbuna sama da 60 zuwa sararin samaniya a shekarar 2023. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)