Kwamitin kula da harkokin harajin kwastam na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata sanarwa a yau Laraba 9 ga wata, wadda ke cewa bayan majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince, tun daga karfe 12 da minti 1 na Alhamis 10 ga watan nan na Afrilun shekarar 2025, an gyara sanarwar kwamitin ta kara yawan harajin kwastam, ga kayayyakin da ake shigarwa kasar daga Amurka, wato an kara yawan harajin daga kashi 34 zuwa kashi 84 cikin dari.
Sanarwar ta bayyana cewa, a ranar 8 ga wannan wata, gwamnatin kasar Amurka, ta sanar da kara buga harajin kwastam ga kayayyakin da ake shigarwa kasar daga kasar Sin, daga kashi 34 zuwa kashi 84 cikin dari.
Kwamitin ya ce, matakin gwamnatin Amurka babban kurkure ne, wanda ya sabawa moriyar kasar Sin, ya kuma haifar da illa ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa tushen ka’idojin cinikayya.
Don haka bangaren Sin ya kalubalanci kasar Amurka da ta gyara kuskurenta cikin hanzari, ta soke dukkan matakan kara buga harajin kwastam kan kasar Sin daga bangare daya, kana ta hau teburin shawarwari tare da kasar Sin, don daidaita matsalolinsu bisa tushen girmama juna. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp