A yau Juma’a ne kasar Sin ta kara ware Yuan biliyan 1.46 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 203.95, don samar da agaji ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, da tabbatar da rayuwarsu ta yau da kullun ya daidaita, kamar yadda ma’aikatar kudi da ma’aikatar ba da agajin gaggawa suka bayyana.
Gaba daya jimilar kudaden da gwamnatin Sin ta ware domin shawo kan ambaliyar ruwa da kuma agaji tun daga farkon farawar ambaliyar ruwa a bana ya kai yuan biliyan 7.74. (Mai fassara: Yahaya)