Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar ta sanya sunayen wasu kamfanonin Amurka 12, cikin jerin sassan da ta haramta a fitar musu da kayayyakin daga kasar Sin.
Sanarwar ma’aikatar ta nuna cewa, tun daga karfe 12:01 na tsakar ranar 10 ga watan Afirilun nan, Sin ta dakatar da fitarwa wadannan kamfanoni nau’o’in kayayyakin da ake iya amfani da su a harkokin soji da kuma fararen hula.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Masunta 3, Sun Sace Dabbobi A Sakkwato
- Amurka Ta Ƙara Wa Kayayyakin China Haraji Zuwa Kashi 104
Kamfanonin da wannan lamari ya shafa sun hada da American Photonics, da Novotech, da Echodyne, da Marvin Engeering, da Exovera, da Teledyne Brown Engineering, da BRINC Drones, da SYNEXXUS, da Firestorm Lab, da Kratos Unmanned Aerial Systems, da Domo Tactical Communications and kamfanin Insitu.
Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni.
Ban da haka kuma, ma’aikatar ta ce kasar ta kara sunayen wasu kamfanonin Amurka 6, cikin jerin sassan da ba za a iya dogaro da su ba.
Ma’aikatar wadda ta bayyana hakan a Larabar nan, ta ce kamfanonin su ne Shield AI, da Sierra Nevada Corporation, da Cyberlux Corporation. Sai kuma Edge Autonomy Operations LLC, da Group W and Hudson Technologies.
Tun daga karfe 12:01 na tsakar ranar gobe Alhamis, takunkumin zai hau kan wadannan kamfanoni, inda za su rasa damarsu ta yin duk wasu huldodin shige da ficen hajoji mai nasaba da kasar Sin, kana an haramta musu zuba duk wani sabon jari a kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp