Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta kaddamar da sauyi a dokar gudanar da rajistar hada hadar cinikayyar kamfanonin kasashen waje, inda dokar ta tanadi kawar da wasu takardun rajista da a baya ake bukata, domin gudanar da kasuwanci ga kamfanonin waje dake cikin kasar, tun daga 30 ga watan Disambar da ya shude.
Karkashin tanadin sauyi, hukumomin da abun ya shafa, sun dakatar da neman takardun rajistar kasuwancin waje, daga kamfanonin dake hada hadar shige da ficen hajoji, da takardun shaidar rajistar fasaha ta kwangilolin shige da fice, da shaidar kayyade hajoji, da takardun shaidar gudanar da kasuwanci na gwamnati, da ma wasu sauran takardu masu nasaba da hakan.
Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta ce wannan sauyi na da matukar muhimmanci ga mamallakan harkokin kasuwancin waje dake kasar Sin. Kaza lika sabon salo ne da gwamnatin Sin ta bullo da shi domin bunkasa cinikayya, da sakarwa kasuwa mara.
Har ila yau, hakan zai taimaka wajen kyautata damar gudanar da kasuwanci a saukake, da ingiza damar bunkasa cinikayyar kamfanonin waje, da bunkasa cinikayya mai nagarta, da kara bude kofa bisa matsayin koli. (Saminu Alhassan)