Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da shirin Japan na aiwatar da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa Sin, ciki har da semiconductor.
Kakakin ya bayyana cewa, shirin bangaren Japan na aiwatar da matakan, zai kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na tsarin masana’antu, da gurgunta mu’amalar kasuwanci na yau da kullum dake tsakanin kamfanoni, da kuma lalata muradun kamfanonin kasashen biyu.
- Dangantakar Cinikayya Da Sin Ta Budewa Afrika Kofar Samun Ci Gaba
- Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Mota Ta Kwace A Legas
Sin na fatan kasar Japan za ta ji ra’ayoyin masana’antu, ta kuma gaggauta gyara ayyukan da ta yi bisa tushen kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da moriyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin.
Bugu da kari, ya ce kasar Sin za ta dauki matakan kiyaye hakki da moriyarta.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp