Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, Sin za ta kakabawa wasu kamfanonin sojan Amurka guda biyar takunkumi, kamar yadda dokar yaki da sanya takunkumai ga kasashen waje ta Jamhuriyar Jama’ar Sin ta tanada. Wannan mataki na da nasaba da sabon zagayen sayar da makamai na baya-bayan nan ga yankin Taiwan na kasar Sin da Amurka ta yi, da kuma yin amfani da uzuri daban-daban wajen kakabawa kamfanoni da wasu Sinawa takunkumi, wannan wani babban gargadi ne ga wasu Amurkawa da ke amfani da batun yankin Taiwan na kasar Sin wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.
A cewar kwararrun da abin ya shafa, wadannan kamfanonin soji 5 duk suna da hannu a cikin sabon shirin Amurka na sayarwa Taiwan makamai. A tsakiyar watan Disambar bara, ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa, ta amince da sayar da makamai da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 300 ga yankin Taiwan na kasar Sin. Wannan shi ne karo na 12 da Amurka ta sayar wa Taiwan makamai tun bayan da gwamnatin Amurka mai ci ta hau karagar mulki.
Matakin da Amurka ta dauka ya saba wa manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma tanade-tanaden sanarwar hadin gwiwa guda uku tsakanin Sin da Amurka, musamman ma yarjejeniyar da aka cimma a ranar 17 ga watan Agusta, kuma hakan ya saba wa alkawurran siyasa da shugabannin Amurka suka dauka a taron birnin San Francisco na kasar Amurka tsakanin Sin da Amurka. Wannan ya sake nuna cewa, wasu mutane a Amurka na juya baya da rashin cika alkawari kan batun Taiwan. (Mai fassara: Ibrahim)