Ma’aikatar aikin gona ta kasar Sin ta mika tallafin wasu jirage marasa matuka 5 na kare shuka ga ma’aikatar noma ta kasar Zambia, a wani mataki na bunkasa noma a kasar dake kudancin Afirka.
An gudanar da bikin mika tallafin jiragen ne ranar Talata, a cibiyar nazarin harkokin noma ta Zambia, bikin da ya samu halartar babban jami’in gudanarwa na ofishin jakadancin Sin a Zambia Wang Sheng, da ministan noma na Zambia Reuben Mtolo Phiri.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
- Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
Cikin jawabin da ya gabatar, Wang Sheng ya ce hadin gwiwa a fannin bunkasa noma wani muhimmin bangare ne na bunkasa hadin gwiwar sassan biyu daga dukkanin fannoni. Ya kuma bayyana fatan ganin jiragen sun taimaka wajen inganta yanayin aikin gona a Zambia. Ya ce Sin a shirye take ta ingiza karin ayyukan hadin gwiwar raya noma a Zambia, da fadada fitar da albarkatun noma na kasar zuwa kasar Sin.
A nasa bangare kuwa, Mista Reuben Mtolo Phiri, jinjinawa gwamnati da al’ummar kasar Sin ya yi bisa goyon bayan da suke baiwa kasarsa, yana mai cewa hakan ya nuna zurfin alakar kawance da hadin gwiwa dake gudana a tsakanin sassan biyu.
Phiri ya kara da cewa Zambia za ta ci gaba da yayata manufar sauya akala zuwa amfani da kayan noma na zamani da kara bunkasa fannin na noma.
(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp