Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a yau Alhamis 24 ga watan nan a birnin Beijing cewa, kasar Sin ba ta yi shawarwari ko tattaunawa da Amurka kan batun karin kudin harajin kwastam ba, balle ma a ce wai an cimma matsaya.
Guo ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na yau da kullum da aka saba yi, yayin da yake mayar da jawabi ga wasu labarai na baya-bayan nan da aka ji daga Amurka, wadanda ke nuna cewa kasashen biyu suna tattaunawa, kuma nan ba da jimawa ba za su cimma matsaya kan batun karin harajin.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
- Nuna Sassauci Ba Mataki Ne Da Ya Dace Da Warware Yakin Harajin Kwastam Ba
Guo ya ce, duka labarun na kanzon kurege ne, inda ya kara da cewa, Amurka ce ta kaddamar da yakin haraji da kasar Sin, kuma dabi’un da kasar Sin ta nuna a kan lamarin daidai ne kuma a sarari suke.
Ya kara da cewa, “Za mu gwabza yaki, idan yakin ya zama dole, amma kofofinmu a bude suke idan Amurka tana son a tattauna,” kana ya ce, Sin na neman hawa teburin tattaunawa da yin shawarwari ne kawai bisa daidaito, da mutuntawa da kuma samun moriyar juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp