Jiya Laraba, kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta kira taron farko na majalisar cinikayyar kayayyaki na bana a birnin Geneva na kasar Switzerland. A yayin taron, bangaren kasar Sin ya nuna damuwarsa matuka game da mummunan tasirin da manufar karin harajin kwastam ta kasar Amurka za ta haifar wa kasa da kasa, inda ya bukaci gwamnatin Amurka da ta bi dokar kungiyar WTO, don kauce wa illar da manufar za ta haddasa wa tattalin arzikin duniya da tsarin cinikayya a tsakanin bangarori daban daban.
Dangane da wannan batu, mambobin kungiyar WTO guda 46 da suka hada da kungiyar tarayyar Turai wato EU, da kasashen Burtaniya, da Canada, da Japan, da Switzerland, da kuma kasar Chadi da sauransu, sun bayyana cewa, suna mai da matukar hankali kan manufar karin harajin kwastam ta Amurka, suna kuma yin kira ga kasar da ta bi dokar WTO yadda ya kamata.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Kolin CELAC Karo Na 9
- ‘Yansanda Sun Cafke Ƙasurguman Masu Garkuwa Da Mutane 2 A Yobe
Kasar Sin ta ce, karin harajin kwastam da kasar Amurka ta yi ya saba da alkawarin da ta yi wa kungiyar WTO kan daidaita harajinta na kwastam, kana, ya keta ka’idar tallafa wa juna tsakanin mambobin kungiyar WTO. Kasar Sin tana fatan dukkan mambobin kungiyar WTO za su tsaya tsayin daka wajen kare tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, tare da warware sabani a tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari da hadin gwiwa.
A sa’i daya kuma, mambobin kungiyar WTO sun jaddada cewa, za su nuna goyon bayansu ga kungiyar WTO don ta ba da gudummawa kamar yadda ake fatan gani, kana suka yi kira ga dukkanin mambobi da su warware sabanin dake tsakaninsu bisa ka’idojin kungiyar ta WTO. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp