• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Raba Basira Da Karfinta Na Inganta Warware Rikicin Ukraine Ta Hanyar Siyasa

by CGTN Hausa
2 years ago
sin

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

A yau Jumma’a ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda ya yi tsokaci game da wasu abubuwa da suka shafi ayyukan diplomasiyya karo na biyu, wadanda wakilin musamman dake kula da harkokin Turai da Asiya na Sin ya gudanar. Lin Jian ya bayyana cewa, wakilin musamman dake kula da harkokin Turai da Asiya na gwamnatin Sin Li Hui, ya tattauna da bangarori daban daban, kan yadda za a gaggauta tsagaita bude wuta, da kuma inganta warware rikicin siyasa da sauransu, yayin da ya ziyarci kasashen Rasha da Ukraine, da sauran wasu kasashen Turai da batun ya shafa.

Bangarori daban daban sun yaba wa bangaren Sin, bisa kokarinsa na gudanar da aikin shiga-tsakani, sun kuma yi imani cewa, a matsayin kasa mai kujerar dindindin a MDD kuma kawa ga Rasha da Ukraine, Sin za ta iya mika sakonni tsakanin kasashen biyu, har da sauran bangarori daban daban, ta yadda za a ingiza dukkan bangarorin su nemi matsaya guda, tare da kiyaye bambance-bambance tsakaninsu, da tattara muradu masu kyau don gudanar da tattaunawar zaman lafiya.

Game da ziyarar da firaministan Eswatini Russell Dlamini ya kai yankin Taiwan a kwanan nan, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin na matukar adawa da keta manufar kasar Sin daya tak da kuma ikon mallakar yankunan kasar.

Har ila yau, game da sanarwar da kungiyar EU ta fitar, a fannin yin rajistar kwastan kan motoci masu amfani da lantari da ake shigarwa Turai daga kasar Sin, wanda ake ganin mai yiwuwa a sanya musu “Harajin kwastan mai tsauri”, da kuma batun da ake yi cewa kasashen Birtaniya da Amurka na shirin gudanar da bincike mai nasaba da tsaron kasa, kan ababen hawa masu aiki da lantarki da ake kerawa a kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, motocin dake amfani da wutar lantarki bangare ne na masana’antar kasa da kasa, kuma ba za a samu nasara ba har sai an yi hadin gwiwa, kana ba za a samu ci gaban fasahohi ba, har sai an gudanar da takara cikin adalci.

Ya kara da cewa, ba da kariya ga cinikayya ya karya ka’idar tattalin arzikin kasuwanni, da kuma kungiyar cinikayyar kasa da kasa. Kaza lika a nan gaba, wannan zai gurgunta moriyar masana’antu, da masu sayayyar kasa da kasa, kana zai yi mummunan tasiri ga sauyin tattalin arzikin duniya maras gurbata muhalli, da kuma kokari na tinkarar sauyin yanayi. (Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Da Wuya Bankuna 17 Cikin 24 Su Mallaki Sabon Jari Da CBN Ya Tsara -Rahoto

Da Wuya Bankuna 17 Cikin 24 Su Mallaki Sabon Jari Da CBN Ya Tsara -Rahoto

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.