Ranar 16 ga watan Afrilu na bana, rana ce ta cika shekaru 31 da kasar Sin ta tura sojoji don shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, a matsayin kasar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD mafi tura ma’aikatan kiyaye zaman lafiya, kuma kasa ta biyu da ta fi zuba kudi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kasar Sin ta riga ta kasance muhimmin bangare a ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.
Wang Wenbin ya yi bayani da cewa, a cikin shekaru 31 da suka gabata, Sin ta tura ma’aikatan kiyaye zaman lafiya fiye da dubu 50, wadanda suka shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya kimanin 30 a kasashe da yankuna fiye da 20, inda cikinsu 25 suka mutu a bakin aiki.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, tabbatar da ka’idojin kundin tsarin mulkin MDD, da sa kaimi ga samun zaman lafiya a duniya da neman makomar bai daya ta dan Adam, su ne burin kasar Sin yayin da take shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Kana kasar Sin za ta ci gaba da bin ra’ayoyin bangarori daban daban, da kiran tabbatar da tsaron duniya, da kuma samar da gudummawarta da dabarunta wajen kawo wa dan Adam zaman lafiya da kuma kyautata tsarin tabbatar da tsaron duniya. (Zainab)