Kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS ya gudanar da taron manema labarai da safiyar yau Jumma’a, don fayyace ruhin cikakken zama na hudu na kwamitin kolin na 20 a birnin Beijing na Sin.
Yayin taron, mataimakin darektan ofishin kula da harkokin yau da kullum na hukumar kula da harkokin kudi da tattalin arziki ta kwamitin kolin JKS, kana darektan hukumar kula da aikin gona ta kwamitin kolin Han Wenxiu, ya ce, shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar na tsara shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, wanda babban taron ya zartas da shi, ya fayyace manyan manufofin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma da za a samu a fannoni bakwai, cikin shekaru biyar masu zuwa.
- Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
- Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya
Na farko, ana sa ran ganin ci gaba mai inganci a kasar zai haifar da kyawawan sakamako. Na biyu, za a inganta yanayin dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha. Na uku, za a sami sabbin ci gaba wajen zurfafa gyare-gyare a bangarori daban daban. Na hudu, za a inganta fannin al’adu da wayewar kan al’umma matuka. Na biyar, za a ci gaba da kyautata rayuwar jama’a. Na shida, za a sami babban ci gaba a fannin kare da inganta muhallin kasar. Na bakwai kuma, za a kara karfafa tsaron kasa.
Bugu da kari, Han ya ce, zamanantar da aikin gona da raya yankunan karkara tana da matukar muhimmanci a cikin aikin zamanantarwa irin ta kasar Sin, saboda haka ya kamata a ba wannan bangare fifiko. Ya ce shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar na jaddada bukatar mai da raya harkoki masu alaka da aikin gona da raya yankin karkara da kyautata rayuwar manoma, a matsayin abu mai matukar muhimmanci, da tabbatar da bunkasar birane da yankin karkara na bai daya, da kuma hanzarta wajen inganta karfin kasar a fannin raya aikin gona.
A yayin taron, direktan hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin, Mr. Zheng Shanjie ya bayyana cewa, “kirkira da habaka sabbin abubuwa” na nufin habakawa da karfafa sabbin masana’antu da masana’antun da za su bullo a nan gaba. A shekarar 2024, tattalin arzikin “sabbin abubuwa uku” (wato sabbin masana’antu da sabbin nau’o’in cinikayya da sabbin hanyoyin kasuwanci) na Sin ya kai kashi 18% cikin alkaluman GDP na kasar. Shawarar da kwamitin tsakiyar JKS ya gabatar game da shiri na 15 na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na shekaru biyar-biyar, ya yi kira da a kirkiro sabbin masana’antu masu muhimmanci, da gaggauta habaka gungun masana’antu masu muhimmanci kamar sabbin makamashi, sabbin kayayyakin aiki da bangaren harkokin sararin samaniya, da tattalin arzikin kasa, wanda zai haifar da kasuwanni da darajarsu za ta wuce Yuan tiriliyan 1. Kazalika shawarar ta yi kira da a shirya da wuri don kafa masana’antu na nan gaba, kamar ta fasahar lissafi ta quantum da kirkirar kayayyakin halitta da makamashin hydrogen da na nukiliya da hada kwakwalwar bil adam da na’ura da fasahar wayar hannu na zamani, da sauransu, wadanda za su zama sabbin hanyoyin habaka tattalin arziki. Wadannan masana’antu a shirye suke don kara karfi wajen kokarin habaka masana’antar fasaha a nan kasar Sin, a cikin shekaru 10 masu zuwa.
Ministan kula da cinikayya na kasar Sin Wang Wentao ya bayyana a yau Juma’a cewa, kasar za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 5, na 15.
Wang Wentao ta kara da cewa, tsakanin shekarar 2026 zuwa ta 2030, za a yi kokarin fadada ba da damar shiga kasuwa da bangarorin da za a kara bude wa kofa, a bangaren bayar da hidimomi. Ministan ya ce wadannan na cikin shawarwarin da kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya gabatar wajen tsara shirin na 15 dake da burin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, wanda aka amince da shi yayin zama na 4 na kwamitin kolin da aka kammala jiya Alhamis.
A cewarsa, sauran manyan ayyuka sun hada da raya sabbin harkokin cinikayya da samar da karin hanyoyin zuba jari tsakanin Sin da kasa da kasa da kuma daukaka hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Safiyah Ma, Amina Xu, Fa’iza Muhammad Mustapha)












