Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudi har yuan biliyan 1.015, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 142 ga lardunan kasar daban daban, domin gudanar da ayyukan jin kai, sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassan kasar.
Rahotanni na cewa ma’aikatar kudin kasar, da ma’aikatar gona da raya karkara, da ma’aikatar albarkatun ruwa ne suka samar da kudaden, wadanda za a yi amfani da su a ayyuka daban daban na tallafawa yankunan da ambaliyar ta shafa, ciki har da birnin Beijing, da lardin Hebei, da Mongolia ta gida da Guangdong. Kana cikin kudin za a samar da tallafin sake shukar da ruwa ya lalata, da ma kayayyakin aikin gona da ambaliyar ta shafa.
Kazalika, za a yi amfani da bangaren kudin wajen tallafin shawo kan fari a lardunan Shandong, da Henan, da Hubei da wasu karin sassan kasar, ta hanyar bayar da tallafin taki, da adana irin shuka, da ban ruwa domin noman rani da tona rijiyoyi. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp