Hukumar kula da kasuwanni ta kasar Sin ta sanar a yau Jumma’a cewa, tun daga farkon shirin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 da ya faro daga 2021 zuwa 2025, kasar ta samu karuwar kamfanoni kusan miliyan 20.
A yayin wani taron manema labarai na bayyana nasarorin da kasar ta samu a tsakanin wannan lokaci, shugaban hukumar Luo Wen, ya yi bayanin cewa, tun bayan kaddamar da shirin na shekaru biyar karo na 14, yanayin kasuwanci na kasar Sin ya ci gaba da habaka, ta yadda aka samu cikakken ci gaban harkokin kasuwanci a tsakanin al’umma.
Luo ya kara da cewa kasar ta kuma samu karuwar iyalan ‘yan kasuwa da suka zamo masu dogaro da kansu miliyan 34 a cikin wadannan shekaru biyar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp