Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa.
Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH da Illumina a cikin jerin kamfanonin da ba su da tabbas. Kana na uku, kasar Sin ta shigar da kara kan matakan da Amurka ta dauka na karin haraji a bangaren sasanta rikici na kungiyar kasuwanci ta duniya, watau WTO.
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 5 A Kaduna.
- Dakarun Sojin Sama Na PLA Sun Yi Shawagin Sintiri A Tsibirin Huangyan
Kazalika, a gefe guda kuma, kasar Sin ta ba da sanarwar hana fitar da kayayyakin da suka shafi sinadaran hada kayayyakin lantarki da karafa na ‘tungsten’, da ‘tellurium’, da ‘bismuth’, da ‘molybdenum’, da kuma ‘indium’.
Bayan haka, duk dai a yau Talatar, hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana cewa, ta kaddamar da bincike kan kamfanin Google na Amurka, bisa zargin keta dokar hana kane-kane ta kasar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)