Kungiyar ciniki ta duniya wato WTO, ta gudanar da taron kwamitin samar da ci gaba da kasuwanci a birnin Geneva na kasar Switzerland, a ranar 17 ga watan nan na Nuwamba. Wakilin kasar Sin ya sanar da taron cewa, Sin da jamhuriyar Kongo, sun rattaba hannu kan ci gaban matakin farko na yarjejeniyar bunkasa huldar abota ta yin hadin gwiwar tattalin arziki a farkon wannan wata.
Wakilin na Sin ya bayyana cewa, a watan Yuni na bana, Sin ta sanar da niyyarta ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar raya tattalin arziki, don aiwatar da matakin cire harajin kashi 100 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigarwa kasar ta Sin daga kasashen Afirka 53 wadanda suke da alakar diflomasiyya da ita.
Rattaba hannu kan yarjejeniyar, wani mataki ne na zahiri na aiwatar da matakin cire harajin, wanda ya dace da ka’idojin WTO. Ya ce a yanayin da kasuwancin duniya ke fuskantar sauye-sauye, Sin tana son more damammakinta na manyan kasuwanni, da samun ci gaba, wajen tallafawa kasashen Afirka su shawo kan kalubale.
A nasa bangare kuwa, wakilin jamhuriyar Kongo ya bayyana cikakken goyon bayan ga yarjejeniyar. Yana mai cewa wannan babban mataki ya shaida aniyar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta, a fannin karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kuma ya zama abin koyi ga zurfafa ciniki tsakanin mabambantan bangarori. (Amina Xu)














