A jiya Laraba ne mataimakin ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya sanya hannu kan yarjejeniyar karewa, da wanzar da amfani da mabanbantan albarkatun halittun teku a matakin kasa da kasa, karkashin yarjejeniyar MDD mai alaka da kare teku. Ma ya sanya hannu kan yarjejeniyar ne a madadin gwamnatin kasar Sin, a helkwatar MDD dake birnin New York.
Yarjejeniyar ta kunshi mallaka, da rarraba albarkatun asalin halittun teku, da kafa yankin kare halittun teku, da aiwatar da binciken yanayin muhalli, da gina kwarewa, da gabatar da fasahohin teku, duka dai da nufin kara kafa ka’idojin jagorancin albarkatun teku na duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp