Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin za ta ci gaba da yayata hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik, karkashin cikakkiyar yarjejeniyar yankin ta RCEP, a dukkanin fannoni bisa yanayi mai karko, tare da goya bayan daga darajar manufar cinikayya cikin ’yanci a yankin, ta yadda za a kai ga cimma nasarar samun ci gaba da wadatar bai daya. Jami’ar wadda ta bayyana hakan a jiya Juma’a, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce a ranar Larabar da ta gabata aka yi bikin cikar yarjejeniyar RCEP shekaru 3 da kafuwa.
Da take amsa tambaya game da nasarorin da aka cimma karkashin yarjejeniyar cikin shekaru ukun da suka gabata, da ma hasashen Sin don gane da makomar ci gabanta, Mao Ning ta ce RCEP ta kasance yarjejeniyar gudanar da cinikayya marar shinge mafi girma a duniya, wadda ta kunshin adadin al’ummu mafiya yawa a duniya, wadda kuma ke da makoma mai haske ta bunkasa sama da sauran takwarorinta.
Ta ce yarjejeniyar ta sanya karsashi mai karfi ga dunkulewar tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik, ta samar da damammaki na raya kasuwanni ga kasashe mambobin ta, tare da karfafa gwiwar sassan kasa da kasa kan manufar cudanyar sassa daban daban. (Saminu Alhassan)