Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da MDD, wajen aiwatar da shawarar nan ta tsarin shugabancin duniya ko GGI da Sin din ta gabatar, tare da dafawa wajen gina salon jagorancin duniya bisa adalci da daidaito tsakanin dukkanin sassa.
Li Qiang, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin ganawa da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a gefen babban taron mahawara na MDD karo na 80 dake gudana yanzu haka.
- Collins Whitworth Zai Kafa Tarihin Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Kakkaɓe Masu Amfani da Takardun Bogi a Ma’aikatunta
Li, ya ce cikin shekaru sama da 80 da suka gabata, MDD ta taka rawar gani da ba za a iya maye gurbinta ba a fannin wanzar da zaman lafiya da tsaro, da raya tattalin arziki da zamantakewar bil’adama, tare da kare hakkokin dan Adam.
Daga nan sai ya jaddada aniyar Sin, ta ci gaba da goyon bayan matsayi da ikon MDD, tare da mara baya ga sassan kasa da kasa wajen cimma nasarar amfani da dandalin MDDr a matsayin fagen karfafa shawarwari da hadin gwiwa, da tsare-tsare da aiwatar da matakai yadda ya kamata.
Haka kuma, a yayin zantawarsa da shugabar taron MDD karo 80 Annalena Baerbock, a gefen babban taron muhawarar majalissar dake gudana a halin yanzu, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin na goyon bayan gina MDD mai karin inganci da hangen nesa, ta hanyar gudanar da sauye-sauyen kyautata karko da nagartar ayyukanta. Ya kuma bayyana kakkarfan goyon bayan Sin ga ikon MDD, da rawar da take takawa a harkokin kasa da kasa.
Bugu da kari, a jiya Laraba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai ta EU Ursula von der Leyen a birnin New York.
Yayin ganawar tasu Li Qiang ya ce, a bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kungiyar EU, kuma kasar Sin na fatan kungiyar EU za ta dauki matakai yadda ya kamata, da nufin inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu don tallafa wa al’umma. Haka kuma, ya ce, kasar Sin na fatan kungiyar EU za ta cika alkawarinta na bude kasuwannin cinikayya da zuba jari, da kuma bin ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, da kaucewa shigar da siyasa da batun tsaron kasa cikin harkokin cinikayya.
Ya ce a matsayisu na manyan bangarori guda biyu a harkokin duniya, ya kamata kasar Sin da kungiyar EU, su sauke nauyin dake wuyansu, tare da ba da gudummawa a harkokin kasa da kasa, domin kare moriyarsu da ta gamayyar kasa da kasa.
A nata bangare, Ursula von der Leyen ta ce, kungiyar EU tana fatan aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin bangarorin biyu suka cimma a yayin ganawarsu a bana, da kuma warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, ta yadda za a cimma sabbin sakamako a fannonin zuba jari, da kiyaye muhalli, da taimakawa kasashe masu tasowa da dai sauransu. Ta kuma kara da cewa, kungiyar EU ta yaba wa kasar Sin bisa himmarta a fannin fuskantar sauyin yanayi, tana kuma fatan zurfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannin, domin gaggauta aikin kwaskwarimar neman ci gaba ta hanyoyin kare muhalli, da tabbatar da dauwamammen ci gaban duniya.
A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugaban asusun Gates na kasar Amurka wato Bill Gates a birnin New York. Yayin da suke zantawa, Li Qiang ya ce cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta samu gaggarumin ci gaba a fannin kiwon lafiya, ta kuma halarci hadin gwiwar raya kasashen duniya cikin himma da kwazo.
Ya ce kasar Sin tana fatan karfafa hulda tsakaninta da asusun Gates, domin habaka shirye-shiryen hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya a duk fadin duniya, ta yadda za a tallafawa al’ummomin sassa daban daban, yayin da ake ba da gudummawar raya kasa da kasa. Haka kuma, ya ce, ya kamata kasashen Sin da Amurka su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, da kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya, ta yadda za a tabbatar da bunkasuwar duniya cikin lumana.
A nasa bangare kuma, Bill Gates ya ce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Amurka ita ce dangantaka mafiya muhimmanci a duniya, kuma asusun Gates da shi kansa, suna son ba da gudummawa ga aikin karfafa mu’amala tsakanin kasashen biyu, da kuma fuskantar kalubalolin duniya cikin hadin gwiwa. (Masu Fassara: Saminu Alhassan, Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp