Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta soki yunkurin da Amurka ke yi na hana kasashen duniya amfani da sashen harhada na’urorin laturoni na Chips kirar kasar Sin. Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, ta kira yunkurin na Amurka da cin zali daga bangare guda, da baiwa kasuwa kariya, matakin da tabbas zai illata tsarin ayyukan masana’antun kira da rarraba sassan semiconductor na duniya.
Kazalika, kakakin ma’aikatar ya ce a baya bayan nan sashen lura da harkokin cinikayya na Amurka ya fitar da wasu bayanai, ta fakewa da batun wai ana keta dokokin Amurka na fitar da hajoji, da nufin haramtawa sassan kasa da kasa amfani da sassan na’urorin Chips masu kunshe da manyan fasahohin sarrafa bayanai kirar kasar Sin, ciki har da wanda kamfani Huawei na Sin ke kerawa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp