A jiya Litinin ne aka rufe dandalin koli na shekara-shekara na tattaunawa kan bunkasuwa a kasar Sin. Mahalarta taro sun bayyana cewa, gwamnatin Sin na nacewa ga samun ingantaciyyar bunkasuwa, da bude kofarta, ba ma tana kokarin samun ci gaba bisa kuzarinta da boyayyen karfinta ba ne, har ma ta taka rawar gani wajen gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Daraktar asusun ba da lamuni na IMF Kristalina Georgieva, wadda ta halarci taron, ta yi nuni da cewa, “Yanzu haka Sin tana karkata daga samun ci gaba mai sauri zuwa mai inganci. Na yi imani da cewa, niyyar da Sin take da ita ta gaggauta bude kofa, za ta samarwa al’ummar Sinawa karin armashi.”
A nasa bangare kuwa, shugaban bankin duniya Ajay Banga cewar ya yi, Sin tana kokarin zamanintar da tattalin arzikinta, matakin dake da bukatar kirkire-kirkire, da bunkasa sana’o’i ba tare da gurbata muhalli ba. Kaza lika Sin na matsayin kasa mai karfin tattalin arziki, inda saurin karuwar GPDn ta ya kai kimanin 5%, kuma gudunmawar da take baiwa bunkasuwar tattalin arzikin duniya ya kai kaso 30%.(Amina Xu)