Ma’aikatar kula da ilimi a Sudan ta kudu ta karbi gudummawar littattafai sama da 330,000 daga gwamnatin kasar Sin, wadanda yara ’yan ajin farko a firamare za su yi amfani da su a sassan kasar.
An tsara litattafan ne domin koyar da darussan Turanci, da lissafi da kimiyya, an kuma mika su ga Sudan ta kudun karkashin zango na 2, na shirin tallafin kasar Sin, na hadin gwiwar samar da kwarewa a fannin ilimi.
Da yake karbar tallafin a jiya Laraba, yayin bikin da aka gudanar a birnin Juba, ministan ma’aikatar ilimi a Sudan ta Kudu Awut Deng Acuil ya ce, “A yau muna matukar godiya bisa karbar wadannan kayan karatu, karkashin manufar bunkasa harkar ilimi. Sudan ta kudu na kara azama wajen kyautata tsarin ilimi, da horas da dalibai bisa kwarewa a matakin makarantun raino, da na firamare, da sakandare, da ma fannin ilimin sana’o’i, wanda hakan darasi ne da muka samu, daga tsarin ci gaban ilimin kasar Sin cikin gwamman shekaru.”
A nasa jawabin kuwa, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu Ma Qiang, cewa ya yi nasarar da aka samu a zangon farko, na aiwatar da manufar tallafin kasar Sin bisa hadin gwiwar samar da kwarewa a fannin ilimi a shekarar 2018, ta share fagen bunkasa cikakkiyar hadin gwiwar raya ilimi a kasashe masu tasowa.
Ma Qiang ya kara da cewa, karkashin zango na 2 na shirin, koyar da yaren Sinanci da darussan raya al’adu, sun bunkasa musaya, da kara fahimtar juna tsakanin al’ummun kasashen biyu. (Saminu Alhassan)