Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin 11 ga wata cewa, kasarsa ta yaba da wasu shawarwarin da aka fitar cikin “matsayar da aka cimma tsakanin Sin da Afirka a Dar es Salaam”, tare da bayyana fatanta da yin kokari tare da kasashen Afirka, don taimakawa ci gaban duniya cikin adalci, kunshe da bangarori daban daban, da ingiza habakar tattalin arzikin duniya ta hanyar dunkule tattalin arzikin duniya baki daya.
A wajen taro na 13 na dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya, kwararru da masanan kasar Sin da kasashen Afirka sun fitar da ra’ayi daya da aka cimma tsakaninsu, dangane da zurfafa hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin samar da ci gaba.
Game da wannan batun, Wang Wenbin ya ce, wannan “ra’ayi iri daya”, yana kira ga kasa da kasa da su zurfafa hadin-gwiwa don samar da ci gaba, bisa manufofin girmama juna, da inganta hadin-gwiwa, da cimma moriya tare, da samar da bunkasuwa tare. Haka kuma yana bayyana cewa, ya dace a bi akidar samar da ci gaba bisa tushen al’umma, da kirkiro wani kyakkyawan tsari da muhalli ga jama’a don su ji dadin rayuwa. Har ila yau, ra’ayin ya jaddada cewa, ya zama dole a yi shawarwari tsakanin mabambantan al’ummu, ba tare da tayar da rikici ba, da girmama al’adun gargajiya da tarihi gami da hakikanin halin da al’ummomi daban-daban ke ciki, tare kuma da nuna goyon-baya ga kasashe daban daban, don su bi tafarkin zamanantar da kansu daidai da bukatunsu. (Murtala Zhang)