Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, a yau Talata ya yi watsi da ikirarin da Amurka ta yi na cewa kasar ta Sin na karya yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin kasashen biyu a tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci da aka yi a Geneva, inda ya bukaci Amurka da ta daina yada labarun kanzon kurege.
A yayin taron manema labarai na yau da kullum, Lin ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace, tare da daukar yarjejeniyar da aka cimma a shawarwarin Geneva da muhimmanci, tare da aiwatarwa yadda ya kamata.
- Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya
- Sallah: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Naira Miliyan 337 Ga Mata 11,229
Bugu da kari, Lin ya ce, Amurka ta yi matukar kawo cikas ga yarjejeniyar, ta hanyar daukar matakan nuna wariya da dama a kan kasar Sin, ciki har da fitar da tsare-tsaren hana fitar da kayayyakin fasahar sadarwar kirkirarriyar basira, watau AI Chip, da dakatar da sayar da zayyanar manhajar kayayyakin fasahar ta AI Chip ga kasar Sin, da kuma sanar da soke biza ga daliban kasar Sin.
Yayin da yake jaddada cewa matsin lamba da tilastawa ba su ne hanyoyin da suka dace na mu’amala da kasar Sin ba, jami’in ya bukaci Amurka ta mutunta hakikanin gaskiya, da dakatar da yada labarun kanzon kurege, kana ta gyara kura-kuranta, da kuma daukar kwararan matakai na kiyaye yarjejeniyar da aka cimma yayin tattaunawar Geneva. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp