Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasarsa ta damu matuka kan yadda zaman dar-dar da tashe-tashen hankula ke ci gaba da karuwa a tsakanin Falasdinu da Isra’ila, inda ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su kwantar da hankulansu, su kuma yi taka-tsantsan, tare da gaggauta kawo karshen tashin hankalin, don kare fararen hula, da kaucewa karuwar tabarbarewar halin da ake ciki.
Kakakin ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani, ga kazamin rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da kungiyoyin Falasdinawa masu dauke da makamai a zirin Gaza, wanda ya haddasa hasarar dimbin rayuka tsakanin sassan biyu.
- Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau
- Aikin Raya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ya Samar Da Sabbin Damammaki Ga Duniya A Cewar Kusoshin Siyasa Na Kasashe Da Dama
Ya ce, sake barkewar rikicin ya sake nuna cewa, lafawar zaman lafiya da aka samu, ba zai dore ba. Don haka, hanya mafi dacewa ta fita daga rikicin ta ta’allaka ne wajen aiwatar da shawarwarin kafa kasashe biyu da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Kakakin ya ce, akwai bukatar kasashen duniya su dauki matakin gaggawa, da kara kaimi kan batun Falasdinu, da shirya fara tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila, tare da samar da hanyar wanzar da zaman lafiya mai dorewa.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tukuru tare da kasashen duniya ta wannan fuska. (Ibrahim)