ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dagwalon Nukiliyar Japan: Kar Duniya Ta Rungume Hannu Kilu Ta Ja Bau

by Abdulrazaq Yahuza
3 years ago
Japan

A ranar 24 ga Satumbar da ta gabata ce aka cika wata guda da fara zubar da dagwalon tashar Nukiliyar Fukushima ta Japan a cikin Tekun Pacific, lamarin da ya haifar da tir da Allah-wadai da kuma fargabar illar da abin zai yi ga rayuwar bil’adama a doron kasa da kuma halittun da ke cikin ruwa.

A ranar Juma’a 22 ga Satumba, firaministan tsibiran Solomon Manasseh Sogabare ya yi Allah wadai da zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Japan a cikin teku, ya bayyana hakan a matsayin wani hari kan amana da hadin kan duniya. “Rahoton tantancewa na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ba ta cika ba, kuma bayanan kimiyyar da aka fitar ba su wadatar ba, kuma suna cike da son zuciya, yayin da aka yi watsi da wadannan damuwar,” a cewar sa. Firamininstan ya ci gaba da cewa, Idan ruwan dagwalon nukiliyar ba ta da hadari, kamata ya yi Japan ta adana ruwan a kasarta, kasancewar an zubar da ruwan dagwalon a cikin teku na nuni da cewa tana da hadari.

  • Hadin Gwiwa Tsakanin Masana’antar Sarrafa Karfe Ta HBIS Da Ta Smederevo
  • Ambaliyar Ruwa: Jihohi Sun Yi Watsi Da Kiraye-kirayen Hukumomi

Dagwalon da Japan ke zubarwa da adadinsa ya haura sama da tan miliyan daya daga ranar 24 ga Agustan 2023, ana iya shafe kimanin shekara 30 ana yi ba a kammala ba.

ADVERTISEMENT

Adawa da abin da Japan ke yi daga masu ruwa da tsaki kan sha’anin teku ya tabbatar da kin amincewa da ikirarin gwamnatin kasar na cewa an tsaftace dagawalon. Daga cikin gida, wani gungun mazauna kasar a karkashin Majalisar Hulda da Jama’a ta kasa da ke adawa da zubar da dagwalon masana’antun makamashin nukiliya, sun shigar da kara a ofishin Gundumar Tokyo. Inda suka zargi Firayim Minista Fumio Kishida da Shugaban Kamfanin Lantarki na Tokyo (TEPCO) Mista Tomoaki da nuna sakaci kan wannan al’amari.

Masu koken sun bayyana cewa dagwalon na dauke da makamashi mai guba baya ga sinadarai masu hadari da ke narkewa wanda ba zai yiwu a raba shi da dagwalon ba ko da bayan an tsaftace shi. Suka kara da cewa har yanzu wannan babbar barazana ce ga kiwon lafiyar dimbin mutanen da suke cin naman dabbobin ruwa.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Har ila yau, akwai masana kimiyya da suka nuna shakku game da rashin hadarin dagwalon da Japan ke zubarwa. A rahoton da Kungiyar Masu Zurfafa Binciken Kimiyya ta Amurka da ke Birnin Washington, ta wallafa a 2021, ta ce akwai yiwuwar a samu wasu sinadaran makamashi masu guba da ke daukar tsawon lokaci ba su narke ba, da za su iya silalewa yayin gudanar da aikin tsaftace dagwalon.

Bugu da kari, a mukalar da ya rubuta, mai taken “Shin dagwalon Fukushima ba shi da hadari? Abin da kimiyya ta ce” da aka buga a Mujallar “Nature” cikin watan Yuni, masanin halittun ruwa, Mista Robert Richmond daga Jami’ar Hawaii ya yi tambaya: “Shin mutanen da ke sahihantar da wannan (fitar da dagwalon makamashin nukiliya na Japan)… sun nuna gamsuwarmu ne cewa zai kasance ba tare da wani hadari ba ga lafiyar Dan’adam da kuma teku? “Amsar ita ce a’a,” in ji Richmond.

Shi ma daya daga cikin masana kimiyya biyar na kwamitin ba da shawara ga Dandalin Tsibiran Pasifik, Richmond ya ce bayan nazarin bayanai daga Kamfanin Lantarki na TEPCO da Gwamnatin Japan, da kuma ziyartar tashar nukiliyar Fukushima, ba a magance zargin da ke cikin fitar da dagwalon ba.

Bisa bayanan masanan, zubar da dagwalon a teku zai haifar da mummunar illa ga muhalli da za a dade ba a magance ba, sakamakon makamashi da sinadarai masu hadari ga halittun ruwa da ‘yan adam musamman masunta da mutanen garuruwan da ke gabar teku.

Bayanai na nuna cewa damuwar da aka shiga kan zubar da dagwalon ta jefa shakku a zukatan mutane musamman wadanda ke zama a kusa da tashar Fukushima game da abin da gwamnatin Japan ke yi, sakamakon har yanzu ba su manta da yadda aka yi tafiyar hawainiya wajen sanar da su bayanan da suka kamata ba bayan ibtila’in da ya auku a 2011.

Masu kare hakkin Dan adam na Majalisar Dinkin Duniya su ma sun nuna adawa da abin da Japan ke yi, haka su ma masu rajin kare lafiyar muhalli. Kungiyar Kare Lafiyar Muhalli ta Greenpeace ta fitar da rahotannin da suka nuna shakku a kan matakan da Kamfanin TEPCO ke amfani da su wajen tsaftace dagwalon, inda ta yi zargin cewa ba a zurfafawa ta yadda za a magance illar da abin ka iya haifarwa.

Ita ma Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta da zubar da dagwalon na Japan a teku. Rahotanni sun nuna cewa tuni kasar ta dauki matakin rage yawan abincin da ake samu daga teku da kasar ke sayowa daga Japan.  A kasar Koriya ta Kudu ma, wani sauraron ra’ayoyin jama’a da aka gabatar kwanan baya, ya nuna kashi 80 cikin 100 na mutanen kasar sun nuna damuwa kan fitar da dagwalon.

Wasu na iya tunanin cewa, watakila Japan ba ta da zabi ne illa ta antaya dagwalon a teku, sai dai kuma ba haka ba ne. Wani babban masanin kimiyya a Cibiyar Binciken Kimiyyar Teku da Muhalli ta Woods Hole Oceanographic da ke Birnin Massachusetts na Amurka, Mista Ken Buesseler, ya ce kamata ya yi Japan ta zubar da dagwalon a kan-tudu, “domin zai fi saukin sa ido da kula da abubuwan da ka iya haifarwa.” Haka nan da an hada da zabin gauraya dagwalon da kankare wajen fitarwa.

Matukar kasashen duniya suka rungume hannu suka bari wannan dabi’a ta Japan ta ci gaba, tabbas kilu za ta jawo bau, domin kamar yadda Mista Buesseler ya nuna fargaba a kai, abin da Japan ke yi na iya bude kofa ga wasu kasashe ta zubar da dagwalon nukiliyarsu a teku. Riga-kafi dai ya fi magani!

Japan
Abdulrazaq Yahuza
+ postsBio
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Halaye 8 Na Rayuwa Da Aka Fi So A Yi Shiru Maimakon Magana (2)
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Halaye 8 Na Rayuwa Da Aka Fi So A Yi Shiru Maimakon Magana A Ciki 
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Saudiyya Ta Taya Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
NNPP Ba Za Ta Rasa Kujerar Gwamna A Kano Ba – Aniebonam

NNPP Ba Za Ta Rasa Kujerar Gwamna A Kano Ba – Aniebonam

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.