A yayin da ake tattauna batun kasar Sudan ta Kudu a taron kwamitin sulhu na MDD a jiya Laraba, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya bayyana cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su girmama cikakken ‘yanci da shugabancin kasar Sudan ta Kudu a lokacin mulkin rikon kwarya, kuma su kaucewa matsawa kasar lamba, ko kuma tilasta mata yin wani abu bisa ka’idojin kasashen waje.
Dai Bing ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, kasar Sudan ta Kudu tana cikin muhimmin lokaci na aiwatar da yarjejeniyar neman farfadowa da kuma inganta aikin rikon kwarya, kana ya kamata gamayyar kasa da kasa su goyi bayan kasar Sudan ta Kudu don ta sami ci gaba cikin lumana. Ya ce zai fi kyau gamayyar kasa da kasa su taimaki kasar Sudan ta Kudu wajen aiwatar da yarjejeniyar neman farfadowa yadda ya kamata, tare da sa kaimi ga bangarorin adawa na kasa da su yi shawarwari kan harkokin siyasa, da karfafa fahimtar juna a tsakaninsu, gami da cimma matsaya daya kan karin harkokin siyasa, domin gudanar da babban zabe yadda ya kamata.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata a mai da hankali kan kalubalen karancin kudaden gudanar da babban zabe da kasar Sudan ta Kudu take fuskanta, da kuma ba da taimakon kudi da ma sauran taimakon da kasar ke bukata, ta yadda kwamitin zabe, da kwamitin hadin gwiwar sa ido da tantancewa, da dai sauran hukumomin da abin ya shafa, za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Dai Bing ya ce, kasar Sudan ta Kudu tana da yanayinta na musamman, kana, jama’ar kasar suna da ikon tsai da kuduri kan makomarsu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp